Gwamnatin Tarayya ta Bawa Jahar Jigawa N47b

 

Gwamnatin Tarayya ta ba Jihar Jigawa N47b da take binta bashi.

Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar ya tabbatar da wannan jiya.

Biliyan 10 daga cikin kudin sun fito ne daga aikin filin jirgin sama.

Mai girma gwamnan Jigawa ya bayyana cewa jiharsa ta karbi wasu kudinta da ta ke jira daga hannun gwamnatin tarayyar Najeriya.

The Nation ta rahoto cewa Muhammadu Badaru Abubakar ya tabbatar da karbar fiye da Naira biliyan 47 daga hannun gwamnatin tarayya.

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar yace an dawo masu da wannan kudi ne saboda abin da gwamnatin jiha ta kashe wajen gina filin jirgi.

Bayan haka akwai kudin bashin Paris Club wanda gwamnati ta karba da yanzu ya dawo hannun gwamnatin jihar Jigawa, jaridar ta rahoto haka.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba, 2020, wajen kaddamar da titin Balago zuwa Auno mai-cin kilomita 42.

Badaru Abubakar ya ce an ba jiharsa Naira biliyan 37 na bashin Paris Club da gwamnatin tarayya ta karba.

Bayan haka gwamnatin tarayya ta aiko wa jihar Naira biliyan 10 a matsayin abin da ta batar wajen gina filin jirgin sama na jihar Jigawa a Dutse.

Da yake na shi jawabin, shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya yabi gwamnan Jigawa.

Sanata Atiku Bagudu ya ce Badaru Abubakar ya ciri tuta wajen takatsan-tsan a kashe dukiyar al’umma.

Atiku Bagudu yake cewa titin da za a gina daga Balago zuwa Auno zai taimaka wa tattalin arzikin mutanen wannan yanki da sauna al’ummar yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here