Gwamnatin Tarayya Tayi Martani Kan ASUU

 

Gwamnatin tarayya ta musanta maganar da shugaban ASUU yayi a ranar karshen mako.

Ta ce tana kan hanyar cika duk alkawuran da ta daukar wa ASUU, ta ma cika wasu yanzu haka. Sannan sun yi da ASUU cewa za ta janye yajin aikinta a ranar 9 ga watan Disamba kuma za ta biya su albashi.

A jiya ne gwamnatin tarayya ta nuna takaicinta a kan maganganun da shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi yayi a kan yadda yace gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta daukar wa kungiyar.

ASUU ta ce malaman jami’a ba za su koma makarantu babu abinci ba. Amma ministan kwadago da ayyuka, Sanata Chris Ngige ya ce tabbas an cika wasu daga cikin alkawuran da gwamnati ta daukar wa ASUU, Vanguard ta ruwaito.

Ofishin yada labaran ministan yace, “Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin za ta shigar da kwamitin sasanci na yarjejeniyar 2009 sannan kuma ta cika alkawarin da ta daukar wa kwamitin da farfesa Munzali yake shugabanta.

Ana ta kokarin ganin an bayar da naira biliyan 70 da gwamnati ta amince za ta biya ASUU. Sannan shugaban kasa ya amince da kwamitin ziyara da duba ayyukan jami’o’i, amma kwamitin ba za ta fara aiki ba, har sai makarantu sun bude.

“Ana kokarin kammala takardu a ofishin Antoni janar, sannan ministan ilimi a shirye yake da ya zabi ‘yan kwamiti ziyarar.

“Gwamnati ta amince da biyan albashin ma’aikata da sauran kudade ta wani tsari wanda ba zallar IPPIS bane, sannan kuma ana nan ana gwada ingancin UTAS da NITDA kamar yadda ASUU ta bukata. Don haka duk wani alkawari da gwamnati ta dauka ta cika shi.

Hakazalika ministan ya tabbatar wa da duniya cewa sun yi da ASUU cewa za ta janye yajin aikinta a ranar 9 ga watan Disamban 2020, kuma FG za ta biya albashin malamai zuwa ko kuma kafin ranar da suka koma makarantu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here