Gwamnatin Tarayya ta Shigar da Kamfanin Meta a Kotu

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shigar da kamfanin Meta Platforms Incorporated a kotu a Abuja tana neman a biya ta N30bn.

Gwamnatin ta yi karar Kamfanin Meta wacce ta mallaki Facebook, Instagram da WhatsApp ne kan yi wa yan Najeriya talla ba tare da hukumomin kasar sun tantance tallar ba.

Hukumar ARCON mai kula da tallace-tallace a Najeriya ta ce rashin tantance tallar da Meta ke yi a kafafenta ya janyo wa kasar asarar kudin shiga mai yawa.

Abuja – Hukumar kula da talla na Najeriya, ARCON, ta ce ta shigar da kara kan kamfanin Meta Platforms Incorporated (masu Facebook, Instagram da WhatsApp) da wakilin ta AT3 Resources Limited a babban kotun tarayya ta Abuja.

A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Talata, ARCON na neman kotun ta tabbatar da cewa cigaba da yi wa yan Najeriya talla ba tare da hukumar ta tantance tallar ba ya saba dokar Najeriya, kuma haramun ne.

ARCON ta ce cigaba da nuna wa yan Najeriya talla da Meta ke yi ba tare da an tantance su ba na cigaba da janyo wa kasar asarar kudin shiga.

ARCON na neman a biya ta diyar N30bn

Don haka, ARCON ne neman kotun ta tursasa wa kamfanin Meta biyan kudi N30bn saboda cigaba da haskawa yan Najeriya talla da hukumar ba ta tantance ba.

Wani sashi na sanarwar ta ce: “ARCON ta jadada cewa ba za ta amince da talla bai dace ba kuma wanda ya saba tsari a ga yan Najeriya masu amfani da intanet.”

Ba dandalin sada zumunta muka saka wa ido ba, talla muke duba wa – ARCON

A cewar ARCON, hukumar ta tana kokarin sa ido kan dandalin sada zumuntar bane. Amma, ta mayar da hankali ne kan talla da kasuwanci da ake yi a dandalin sada zumuntar na intanet bisa dokar da aka kafa ta a kai.

Dakaci karin bayani ..

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here