Gwamnatin Tarayya Zata Rushe NNPC
Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da cewa za a rusa babban kamfanin na kasar NNPC a cikin sauye-sauyen da za a iya wa fannin man kasar karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur.
Read Also:
Sai dai ta ce za a maye gurbinsa da wani mai zaman kansa.
Wannan na daga cikin ayukkan da aka dorawa kwamitin share fage kan aiwatar da dokar da Shugaban Muhammadu Buhari ya sanar da kafawa a dazu yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.
Ministan albarkatun man fetur Timipreye Silver ne zai jagoranci wannan kwamitin.