Bayan Kwace Mulki: ‘Yan Taliban Sun je Gurin Shaƙatawa

 

Mutane daga sassa daban-daban na duniya suna ta nuna al’ajabi kan jerin wasu bidiyo na mayaƙan Taliban a wuraren shaƙatawar yara da wuraren motsa jiki suna ta tsalle-tsalle.

Bidiyo da hotunan sun yaɗu kamar wutar daji a ranar Alhamis inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu.

Wannan lamari na zuwa ne kwana biyu bayan da ƙungiyar ta gama ƙwace iko da ƙasar daga hannun gwamnati, bayan janyewar dakarun Amurka da suka shafe shekara 20 suna yaƙi.

Babban abin da ya fi bayar da mamakin shi ne yadda ba a saba ganin mayaƙan na Taliban suna duk wani abu da ya danganci wasa ko raha na – sun fi mayar da hankali wajen yaƙi.

Yawo da bindigar AK47 da aka fi saninta da Kalashnikov a Taliban, ita ce alama da ke nuna ƴan Taliban a ko yaushe, saboda ba sa yawo sai da ita.

Don haka ganinsu a irin wannan yanayi na wasa da dariya ya jefa mutane cikin mamaki da tunanin anya ƴan Taliban din da aka sani a baya ne ko kuwa wasu sabbi ne.

Me bidiyon suka ƙunsa?

Bidiyo daban-daban da suka kai huɗu ne suka yaɗu a shafukan sada zumunta.

Na farko yana nuna mayaƙan Taliban din ne dukkansu ba sa ɗauke da bindigar Kalashnikov, sun ajiye su a gefe, a filin wasan yara, wato Amusement Park.

Sun shiga cikin motocin da ake fi sani da Bumper Cars suna ta tuƙawa cikin nishadi suna karo da juna.

Sannan an gan su suna hawa irin dokin nan na wasan yara suna ta sukuwa.

A bidiyon an ga yadda yara da mata da wataƙila suka je wajen shaƙatawar, suna tsaye suna kallon mayaƙan Taliban.

Bidiyo na biyu kuwa, ƴan Taliban aka gani shi ma dai a wajen wasan yara, suna ta tsalle-tsalle a kan wani abu da ake kira Bouncing Castle.

Shi dai Bouncing Castle ana hawa kansa ne a yi ta tsalle ana faɗawa kai kamar dai shillo. Shi ma yawanci yara aka fi gani suna wasa a kai.

Amma a wannan bidiyon sai ga ƴan Taliban ɗin har wasu na ƙoƙarin cire rawaninsu, wataƙila don su fi jin daɗin tsallen da kyau. Suna kuma ta sheƙa dariya.

Bidiyo na uku kuwa nuna ƴan Taliban ya yi a wajen motsa jiki. Sun hau kan abin motsa jikin da ak fi sani da Tred Mill wanda yake yi kamar mutum na tafiya ne a kai.

Sai dai shi a cikinsa ba su cire rawanin ba, amma ga alama wasu ma a tsorace suke da shi don kar su faɗi, wataƙila saboda rashin sabo.

Na ƙarshen kuwa ba a wajen wasa aka ga mayaƙan Taliban din ba. An gansu ne a cikin wani babban falo a fadar gwamnatin Afghanistan.

Sun barbaje a kan kujeru suna kwasar girki, loma ba kama hannun yaro.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here