Kwashe N10m: Hukumar ‘Yan Sandan Jahar Oyo Sun Kama Ma’aikacin Banki

 

Hukumar ‘yan sandan jahar Oyo sun damki wani Adeyemi Tosin, ma’aikacin banki bisa zargin wawurar kudin wani abokin huldarsu dake ajiya a bankin.

Ana zargin Tosin da kwashe naira miliyan 10 daga asusun bankin Oladele Adida Quadri mai shekaru 78 tsakanin ranar 12 ga watan.

Augusta da ranar 13 ga watan Sakamakon bincike ya bayyana yadda Tosin ya bude wani asusu a wani banki na daban yayi ta kwasar kudaden yana zubawa a sabon asusunsa.

Oyo – Hukumar ‘yan sandan jahar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Yadda al’amarin ya kasance

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jahar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

A cewarsa an gano yadda matsalar ta auku bayan ATM ya hadiye katin Quadri a reshensu na Ibadan, Shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Quadri ya nemi taimakon ma’aikacin ne bayan ya shiga bankin inda ya bashi duk wasu bayanansa.

Kamar yadda Tribune Online ta wallafa, wanda ake zargin ya yi amfani da damar ya bude sabon asusu yayi ta wawurar kudaden mutumin yana zubawa a asusunsa.

Yanzu haka ana cigaba da bincike akan wadanda suke da hannu a lamarin, kwamishin ‘yan sandan jahar, CP Ngozi Onadeko ta bukaci mutanen kirkin jahar su hada kai da ‘yan sanda wurin taimakawa a kammala binciken, a cewar Osifeso.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here