Gwamnatin Tarayya ba ta Tallafa Min Wurin Biyan Albashi da Fansho – Gwamna Ortom
Gwamna Samuel Ortom na jahar Binuwai ya zargi gwamnatin tarayya da rashin taimako a gare shi.
Ya ce akwai wadanda suka tallata ma sa shiga jam’iyya mai mulki ta APC amma ya ki shiga saboda mutanen sa.
A cewar sa yanzu haka gwamnatin tarayya ba ta tallafa masa wurin biyan albashi da fansho.
Jahar Binuwai – Gwamnan jahar Binuwai, Mr Samuel Ortom ya jefi gwamnatin tarayya da wani zargi kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.
A cewar Ortom, gwamnatin tarayya tana tura kudi mara yawa ga gwamnatin jahar sa don haka ba ya samun damar biyan albashin ma’aikatan sa yadda ya dace.
Ortom ya ce an yi masa tallar APC
Ya kara da bayyana yadda wasu mutane suka je har inda yake inda suka bukaci ya canja shekar sa ya koma APC, inda ya kara da cewa ba ya samun tallafin da ya dace daga gwamnatin Muhammadu Buhari kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.
Ya kara bayyana cewa naira biliyan 28 da gwamnatin tarayya ta ba shi be ishe shi biyan bashin naira biliyan 70 ba, inda ya kwatanta da sauran kudaden da ake bai wa wasu jahohi.
Kamar yadda Ortom ya bayyana:
Read Also:
“An dade ana cutar dani ana so ayi amfani da wata dama a kai na. Ina yi wa kasar nan fatan alheri shiyasa ake ganin ina amfani da kalolin sutturun wasu yaruke na jihar Binuwai; kamar Tibi, Idoma, Egede ba kalar tutar Najeriya ba. Na yi imani da Najeriya. Karfin mu shi ne hadin kan mu. Kuma na yarda zamu iya taruwa mu yi aiki gabadaya.
“Gwamnatin tarayya ta ki taimakamin wurin biyan kudaden fansho da garatuti wanda na gada daga gwamnatin baya. Ba laifi na bane. Aper Aku ya gaji bashin albashi da garatuti, Adasu ma haka, Suswam ma ya gada gashi nima na gada. Na gaji bashin naira biliyan 70 na kudin fansho, albashi da garatuti. Kuma ba sabon abu bane.
“Gwamnatin tarayya ta bani naira biliyan 28 kuma na yi amfani dasu sai dai bai isa ba. Wasu sun samu amma gwamnati ta ki tallafa min in karasa biyan sauran.
“Mutane sun zo suna ce min idan na koma APC, zasu mara min baya na ce ba zan iya bai wa mutane na kunya ba. Sun zabe ni, bazan so abinda zai sosa musu rai ba kuma matsawar su na baya na zan cigaba da jajircewa akan su. Idan su ka juya min baya ina kake so in je?”
“Ba wai na tsani Fulani bane kawai na tsani karya doka ne. Nan jihar Binuwai bana matsa wa kowa. Na bar kiristoci su yi addinin su haka zalika musulmai ko ma marasa addini. Kowa zai iya yin abinda yake so.”