Gwamnatin Tarayya ta Ware N50b Domin a Rika Gwajin COVID-19 a Jahohin Kasar

Gwamnatin Tarayya ta hada-kai da Gwamnoni da nufin yakar Coronavirus.

Kwamitin PTF ya ce zuwa yanzu sun ba Gwamnonin jihohi Naira biliyan 50

 

Sani Aliyu ya yi kira ga Gwamnoni su yi amfani da kudin wajen yin gwaji Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 a Najeria, Dr. Sani Aliyu ya ce an ba jihohin kasar nan Naira biliyan 50.

Dr. Sani Aliyu ya ce gwamnatin tarayya ta bada wannan kudi ne domin a samu damar kara yi wa jama’a da dama gwajin kwayar cutar COVID-19.

Rahoton ya bayyana cewa Sani Aliyu ya yi wannan bayani ne lokacin da kwamitin PTF ya zauna da manema labarai ranar Talata a garin Abuja.

Aliyu a madadin kwamitin PTF, ya yi kira ga gwamnoni su yi amfani da kudin da ke hannunsu wajen yin abin da gwamnatin tarayya ta bukata. “Jihohi sun samu kaso mafi tsoka na kudin PTF.

A yau, an ba su Naira biliyan 50.” Inji Sani Aliyu. Ya ce:

“Don haka mu na da halin da za mu kara yawan gwaje-gwaje a jihohi, da kuma karin bibiya. Shugaban kwamitin na PTF ya jaddada bukatar samun kudi domin yaki da cutar COVID-19, ya ce har yanzu ba a fara hangen karshen annobar ba.

Sani Aliyu ya kuma bayyana cewa an soma yin gagarumin gwajin kwayar Coronavirus a makon nan.

“A wannan makon aka kara yawan wadanda ake yi wa gwajin COVID-19 a kasar nan. Mu na taya Abuja da Legas murnar yi wa jama’a da-dama gwaji.”

“Asali ma, a Abuja an yi 2% na wadanda mu ka tanada gwaji. Jihohi uku sun kama hanya – Filato, Gombe, da Ribas.” Aliyu ya ce jihohin sun kai 50%.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here