Gwamnatin Tarayya ta Roƙi ƙungiyoyin ƙwadago na Kasa da Kada Su Shiga Yajin Aiki

 

Gwamnatin tarayya ta roƙi haɗakar ƙungiyoyin ƙwadugo na kasar nan da kada su tsunduma yajin aiki kamar yadda suke shirin yi.

Ministan ƙwadago na ƙasar ne ya bayyana haka a ya yin ƙaddamar da majalisar bada shawarwari kan ayyukan ƙungiyoyin ƙwadigo (NLAC).

Ƙungiyoyin ƙwadigon na shirin shiga yajin aiki ne matuƙar ba’a watsar da kudirin dake gaban ‘yan majalisar wakilai ba Gwamnatin tarayya ta roƙi haɗakar ƙungiyoyin ƙwadigon ƙasar nan da kada su shiga yajin aikin da suke shirin yi a kan kudirin mafi ƙarancin albashi dake gaban majalisa.

Ministan ƙwadigo na ƙasar nan, Sanata Chris Ngige, ya yi wannan roƙon a wajen ƙaddamar da majalisar bada shawarwari kan ayyukan ƙungiyar ƙwadigo a Owerri, jahar.

Taron wanda Mataimakin shugaban Ƙasa Prof. Yemi Osinbajo ne ya ƙaddamar dashi ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually) a madadin shugaba Buhari.

Lokacin da yake jawabin ƙaddamarwa, Chris Ngige, ya ce yana goyon bayan haɗakar ƙungiyoyin ƙwadigo kan ƙin amincewa da shirin majalisa.

Amma ya roƙe su da kada su tsunduma yajin aiki domin hakan zai shafi cigaban ƙasa.

Ƙudirin, wanda ke gaban ‘yan majalisar wakilan ƙasar nan na ƙunshe da buƙatar a sake yiwa mafi ƙarancin albashi kwaskwarima, wanda hakan zai rage ƙarfin yarjejeniyar da aka cimma kan mafi karancin albashin.

Ministan ya ƙara da cewa, ba a buƙatar ƙungiyon su gode masa kan matsayar daya ɗauka akan kudirin domin shi kawai ya maimaita matsayar gwamantin tarayya ne.

A bayanin ministan yace: “Duk da cewa wannan majalisar bata aiki na wani lokaci, amma ma’aikatar mu ta kiyaye dokar sauraron koke daga ɓangarori uku.

“Misali lokacin da muka tattauna akan mafi ƙarancin albashi, munyi amfani da tsarin zama da ɓangarori sama da uku waɗan da suka haɗa da; Gwamnati, ma’aikata, masu ɗaukar aiki, da kuma masu buƙatar shiga taron dan kansu.” injishi.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan Najeria (NLC) Ayuba Wabba ya yabawa shugaban ƙasa muhammadu Buhari da ya saka NLAC a cikin doka, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Anashi bangaren shugaban yan kasuwa na ƙasar nan (TUC) wanda mataimakinsa, Quadri Olaleye ya wakilta ya yabawa ministan kasancewar sa namijin gaske kan aikinsa, amma yace zasu cigaba da abinda yakamata har sai komai ya dai-daita.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here