Gwamnatin jihar Zamfara dake Arewa maso yammacin Najeriya, ya fara biyan ‘Yan Kato da gora wadan da ta dauka domin taimakama jami’an tsaro wajen kakkabe aikin barayin shanu da Masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa hadi da Masu kashe mutane ba gyara ba dalili.
Yau sun fara karbar alawus din su na wata wata Kamar yadda Gwamnatin jihar zamfara karkashin jagorancin Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar ya alkawaranta.
Read Also:
Akalla mutane Dari biyar ne ake sa ran zasu amfana da wannan shiri na bayar da alawus duk wata ya ‘Yan kato da gora daga karamar hukumar mulki ta shinkafi daya daga cikin yankunan da yayi fama da tashin hankali a jihar.
Idan za’a iya tunawa akwanakin bayane mai gwamna Zamfara ya dauki ‘yan Kato da gora su dubu takwas da dari biyar don kawo karshen kashe kashe da ya addabi jihar zamfara.
The post Gwamnatin Zamfara ta fara biyan ‘Yan kato da gora alawus appeared first on Daily Nigerian Hausa.