Yadda Gwamnatin Tarayya Zata daƙile Matsalar Tsaron ƙasar nan – Ibrahim Kpotun Idris

Wani tsohon sufetan yan sandan ƙasar nan ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar yadda zata yi ta daƙile matsalar tsaron ƙasar nan da jami’an yan sanda kawai.

Ya ce babu isassun yan sanda a ƙasar nan idan ka kwatanta da yawan jama’ar da Najeriya ke dasu.

A cewar tsohon Sufetan idan har gwamnati ta ɗauki sabbin jami’an yan sanda, sannan kuma ta kula da walwalarsu yadda yakamata to zasu iya magance matsalar tsaro gaba ɗaya.

Tsohon sufetan yan sandan ƙasar nan, Ibrahim Kpotun Idris, yayi kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki sabbin jami’an yan sanda matuƙar tana son ta kawo ƙarshen ƙalubalen tsaron da yaƙi ci yaƙi cinyewa.

Idris yace dalilin da yasa matsalar tsaro take cigaba da ruruwa a ƙasar nan shine saboda rashin isassun jami’an yan sanda da kuma rashin kula da su yadda yakamata.

Tsohon sufetan wanda ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, yace idan ka kwatanta adadin yan sanda da yawan al’ummar Najeriya, zaka tabbatar da babu isassun jami’an yan sanda.

Idris yace

: “Babbar matsalar itace babu isassun yan sanda, jami’an na aiki ne a wahalce idan ka haɗa da yawan al’ummar da muke dashi a Najeriya.

“Na wani ɗan lokaci, inda gwamnati zata ƙara yawan yan sanda domin daƙile matsalar tsaro, to hakan zai taimaka sosai.”

“Haka kuma, yakamata gwamnati ta gyara buƙatun yan sanda, ta ɓangaren walwala da jin daɗinsu da sauran bukatunsu. Matuƙar gwamnati tayi haka to tabbas ƙasar nan zata dawo yadda aka santa.”

“Akwai abubuwa da yawa da yakamata ayi domin ƙara ma jami’an yan sanda ƙarfi, su kuma su sami damar daƙile duk wasu laifuffuka a ƙasar nan.” a cewarsa. Idris ya nuna rashin amincewar sa da shirin ƙirƙiro sabbin jami’an yan sandan jahohi, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Yace ƙirkirar waɗansu jami’ai daban kuma bayan waɗanda ake dasu zai sa tsaro ya ƙara taɓarɓarewa ne kawai. “Maganar jami’an tsaron yankuna, bana tunanin shine hanya mafita, ina ganin sai-dai su rage ma jami’an yan sandan mu karfin gwuiwa, ina ganin ya kamata gwamnati ta dakatar da wannan shirin cikin gaggawa.” inji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here