Gwamnatin Tarayya za ta Kara Albashin Ma’aikata Saboda Halin Matsin Tattalin Arziki – Ministan Kwadago
Ministan Kwadago Da Daukar Aiki, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shawarar karin albashi ga dukkan ma’aikata a Najeriya saboda wahalar rayuwar da ake ciki a fadin kasar.
Read Also:
Ngige ya bayyana hakan yayin da ya gabatar da jawabi a taron kaddamar da littafin cikar kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) shekaru 40 a Abuja, ranar Litinin.
Ministan na kwadago ya ce kara albashin ya zama wajibi saboda halin matsin tattalin arziki da ake zama a fadin duniya, musamman Najeriya.
Ngige yace:
“Hauhawar tattalin arziki ta shafa duniya gaba daya, zamu yi karin mafi karancin albashi bisa abubuwan dake faruwa.”
“Mun fara karin da kungiyar malaman jami’a ASUU saboda yanzu suna tattaunawa da ma’aikatar Ilimi.”