Shugaban Majalisar Dattijai ya Nemi Gwamnatin Tarayya Akan ta Rage Ciyo Bashi

 

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, yace ya zama wajibi a nemo hanyar rage ciyo bashin gwamnatin tarayya.

Lawan ya bayyana haka ne jin kaɗan bayan fitowa daga wata ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban ƙasa.

Sanatan ya kuma musanta zargin da ake yaɗawa cewa majalisa ta karbi na goro domin amincewa da PIB.

Abuja – Shugaban sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana bukatar rage ciyo bashi daga waje ta hanyar toshe hanyoyin karkatar da kuɗaɗen haraji a ma’aikatun gwamnati, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Lawan ya faɗi hakane a fadar shugaban ƙasa yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaba Buhari.

Shugaban sanatocin yace ya zama wajibi gwamnatin tarayya, jahohi da kananan hukumomi su lalubo hanyoyin magance ma’aikatun da basu zuba haraji a asusun gwamnati.

Me manyan shugabannin suka tatauna?

Sanata lawan yace:

“Mun tattauna abubuwan da suka shafi gwamnati, yadda za’a nemo hanyoyin karin kudaden haraji musamman a matakin kasa, jahohi da kuma kananan hukumomi.”

“Akwai ma’aikatun gwamnati da dama dake karkatar da kuɗaɗen haraji ba su zuba su a asusun gwamnati, wannan wata matsala ce da ya kamata a magance ta cikin gaggawa domin muna son rage ciyo bashi.”

“Saboda haka idan akwai hanyoyin da zamu samu haraji sosai, hakan zai taimaka mu rage ciyo bashin da muke.”

“Duk mun amince da wannan da shugaban ƙasa cewa zamu lalubo hanyar kara inganta tattara haraji.”

Kasafin kuɗin shekarar 2022

Shugaban sanatocin ya bayyana cewa sun tattauna kan kasafin kuɗin shekara mai zuwa 2022 da shugaban ƙasa Buhari.

Lawan yace akwai shirin samar da isasshen kaso ga hukumomin tsaro, da kuma wasu ayyuka da aka fara kamar babbar gadar Neja ta biyu, da hanyar Abuja-Kano.

A cewar Lawan sun yi shirin kammala waɗannan ayyukan zuwa shekarar 2022 domin shugaban ƙasa ya kaddamar da su yan Najeriya su amfana.

Shin dagaske majalisa da karbi cin hanci kan PIB?

Sanatan ya musanta zargin cewa majalisa ta karbi dala miliyan $10m domin ta amince da sabon kudirin dokar man fetur PIB.

Ya kara cewa mutane suna magana karangatsai game da shugaban ƙasa, gwamnati da kuma mambobin majalisun tarayya.

“Mutane na kiran mu da sunaye kala daban-daban, kuma kowa yana da damar tofa albarkacin bakinsa amma ina baku shawara ku dinga faɗin alheri.”

“Kwanan nan wani yace an baiwa shugaban sanatoci da kakakin majalisar wakilai dala miliyan $10m su rarrabawa abokan aikinsu dan su gaggauta amincewa da kashi 3% ga yankunan dake samar da man fetur.”

“Wannan abin dariya ne amma shi dagaske yake, saboda haka inason amfani da wannan damar domin nesanta mu da wannan karyar da ake yaɗawa yan Najeriya don bata sunan wasu mutane.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here