Gwamnoni 36: Kisan Manoma 43 ya Nuna Gazawar Tsaron Kasa

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta kwatanta kisan monoma 43 na kauyen Zabarmari a matsayin zalunci.

Sun fadi hakan ne ta bakin shugabansu, inda suka ce harin ya nuna gazawar tsaron kasar gaba daya.

Gwamna Fayemi ya ce wajibi ne su tattauna a kan yadda za su bullo wa lamarin a taron da za su yi na gaba.

Duk gwamnonin jihohi 36 da ke karkashin NGF sun bayyana takaicinsu a kan kisan manoma 43 da aka yi a jihar Borno ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.

A wata takarda da suka saki a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba, wacce shugaban kungiyar, Gwamna Kayode John Fayemi na jihar Ekiti ya fitar, ya ce kisan zaluncin da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka yi, yana nuna zalunci da munin hali irin nasu.

Fayemi ya ce kisan zaluncin yana nuna tsananin gazawar tsaro a Najeriya, domin hakan yana nuna kasawar jami’an tsaro wurin kulawa da rayukan jama’a.

Ya kamata a ce an kara mikewa tsaye don kawo karshen wannan zaluncin. Tsohon CSO tun na mulkin janar Sani Abacha ya bayyana wasu miyagun kudurin wasu shugabannin Najeriya da suke tallafawa wurin baiwa ‘yan ta’adda damar kai hari

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here