Akwai Gwamnonin da Zasu Bar Tafiyar Wike – Dino Melaye
Kakakin tawagar yakin neman zaɓen Atiku Abubakar, Sanata Dino Melaye, yace akwai gwamnonin da zasu bar tafiyar Wike.
Sanatan ya bayyana yaƙinin cewa mai yuwuwa ba dukkansu ba amma wasu daga gwamnonin G5 zasu dawo bayan Atiku.
PDP na fama da taƙaddama a tsakanin mambobinta tun bayan kammala zaɓen fidda gwani a watan Mayu.
Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar PDP da ke tare da gwamna Nyesom Wike, zasu yaudare shi su yi wa ɗan takarra shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, aiki a 2023.
Hakan na cikin ikirarin da mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na PDP (PCC), Sanata Dino Melayw, ya yi a wata hira da Channels tv cikin shirin siyasa a yau.
Rigingimu sun hana zaman lafiya a babbar jam’iyyar adawa tun bayan nasarar Atiku a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa, inda ya lallasa gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.
Read Also:
wike da masu mara masa baya sun ci gaba da hura wuta dole Iyorchia Ayu ya yi murabus daga shugabancin PDP domin ba zai yuwu ya kasance yankinsu ɗaya da Atiku ba.
Duk wani yunkuri da faɗi tashin rarrashinsu ya ci tura har ta kai ga Wike da duk masu goya masa baya sun tsame hannunsu daga kwamitin kamfen Atiku.
Sai dai a halin yanzun, Sanata Melaye, ya bayyana yakininsa cewa duk da sabanin dake tsakani, wasu daga cikin gwamnonin zasu tallata Atiku a babban zaɓe mai zuwa.
The Cable ta rahoto Melaye na cewa:
“Me ya shafi Atiku da saukar Ayu ko zamansa? Tun farko gwamnonin ne suka kawo Ayu matsayin da yake ba tare da shawara ko amincewar Atiku ba. Gwamna Wike ya shige gaba wajen kawo Ayu, Ortom kuma ya tsaya masa.”
Ayu ba ɗan Atiku bane da zai ba shi umarnin ya tafi ya zauna. Bayan haka da Ikon Allah, daga ƙarshe, mai yuwuwa ba dukansu ba amma wasu daga gwamnonin nan zasu yi wa PDP aiki.”
“Ɗaya daga cikinsu, gwamnan Abiya, lokacin da yake jawabi a Makurɗi jiya, yace a zaɓi PDP sak, bai banbanta ba, manufarsa a shirye yake ya yiwa jam’iyyarsa aiki.”