Shugaban APC: Girmamawan da Gwamnoni ke wa Shugaba Buhari Yasa Suke Amince da Zaɓinsa – Gwamna Abdullahi Sule
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce girmamawan da gwamnoni ke wa Buhari yasa suka amince da zaɓinsa.
An kai ruwa rana a jam’iyyar APC tun bayan da shugaban ƙasa Buhari ya nuna wanda yake son ya zama shugaban APC na gaba.
Gwamnan ya ce samun mutum kamar Buhari a jam’iyyar siyasa ba kasafai ba, shiyawa ko wane mamba ke bin umarninsa.
Abuja – Gwamnan jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin Midiya na babban taron APC na ƙasa, Abdullahi Sule, ya yi bayanin abin da yasa gwamnoni suka amince da zaɓin Buhari.
Tribune Online ta rahoto gwamnan na cewa Shugaba Buhari na goyon bayan tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya zama shugaban APC na gaba.
A ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022, APC zata gudanar da babban taronta na ƙasa wanda zata zaɓi shugabanninta.
Da yake jawabi ga manema labarai game da shirin da kwamitinsa ya yi, Gwamna Sule ya ce masu shakku kan zabin Buhari sun amince ne saboda girmamawan da Buhari ke samu daga masu faɗa a ji.
Ya ce:
Read Also:
“Abin da sauran jam’iyyu suka rasa mu muke da shi, shi ne jagoran siyasa kuma Uba, wanda kowane mamban APC yana matukar ganin girmansa, kuma ba kowa bane illa shugaban kasa Buhari.”
“Muna da yaƙinin cewa ba zai taɓa yin abu domin son zuciyarsa ba, ko wani abu daban da zai saɓa wa tsarin jam’iyya. Mutum ne dake sha’awar tabbatar da haɗin kan jam’iyya.”
“Wannan shi ne jagoran da muke da shi wanda duk lokacin da yake jawabi kowa tsif yake ya saurara saboda sun san ba zai yi abu don amfanin kan shi ba. Wannan ne rokon sa, kuma tabbas za’a girmama zancensa.”
Zamu yi kokarin shawo kan sauran yan takara – Sule
Gwamnan ya tabbatar wa ‘ya’yan jam’iyya cewa zasu yi duk me yuwuwa wajen shawo kan sauran yan takara su janye kudirinsu domin cika sharuddan dokar zaɓe.
“Game da kundin dokar zaɓe, jam’iyyar mu ta na bin doka sau da ƙafa, zamu yi abin da ya dace ba tare da sauka daga kan dokoki ba. Ba zamu bari a yi wani abu da zai saɓa wa doka ba a matsayin jam’iyya mai mulki.”
Ya kuma ƙara da ƙarin haske kan shirin kwmaitin rikon kwarya na APC ƙarƙashin jagorancin Mala Buni cewa za’a maida wa yan takarar da suka janye don zaman lafiya kuɗaɗen su.