Wasu Gwamnonin APC Sun Ziyarci Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan

 

Jaridar TheCable ta wallafa rahoton yadda wasu gwamnoni da jagororin jam’iyyar APC suka ziyarci tsohon shugaban kasa; Goodluck Jonathan.

Ana zargin cewa ganawar ba zata rasa nasaba da kulle-kullen takarar shugaban kaasa a zaben shekarar 2023 ba.

An fara zaben Jonathan shugaban kasa a shekarar 2011 kafin daga bisani ya sha kaye a hannun Buhari lokacin da ya nemi zarcewa a karo na biyu.

Gwamnonin jam’iyyar APC sun yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da yammacin ranar Juma’a a Abuja, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Babu wani mamba a jam’iyyar PDP yayin taron. Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, wanda ya koma jam’iyyar APC daga PDP kwanan nan; gwamnan jihar Kebbi; Atiku Bagudu, da takwaransa na jihar Jigawa, Abubakar Badaru.

Duk da babu wanda ya san a kan abinda suka tattuna, TheCable ta ce majiyarta ta kyankyasa mata cewa ganawar ba zata rasa nasaba da kulle-kullen takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 ba.

An fara zaben Jonathan a matsayin shugaban kasa a shekarar 2011 kafin daga bisani ya sha kaye a hannun Buhari a zaben shekarar 2015, amma har yanzu ya na da damar sake tsayawa takara idan ya na so.

TheCable ta yi waiwayen baya tare da zakulo cewa Jonathan ya taba ganawa da Badaru da Bagudu a gidansa da ke Otuoke, jihar Bayelsa, a irin wannan watan da muke ciki na shekarar da ta gabata.

A wancan lokacin, gwamnonin sun ziyarce shi ne domin yi masa godiya a kan goyon bayan da ya bawa dan takarar jam’iyyar APC, David Lyon, har ta kai ga ya samu nasara a zaben kujerar gwamnan Bayelsa a 2019.

Sai dai, daga bisani kotun koli ta kwace nasarar da jam’iyyar APC ta samu tare da mayar da ita hannun jam’iyyar PDP tun kafin a kai ga rantsar da Lyon.

Kafin gwamnonin su ziyarce shi, tsohon shugaban majalisar dattijai, Ken Nmani, tare da wasu sauran jagororin jam’iyyar APC sun ziyarci Jonathan a gidansa domin taya shi murnar cika shekaru 63.

Hatta kungiyar gwamnonin APC na yankin arewa (NGF) sai da ta aikawa Jonathan zungureriyar takardar taya shi murnar cika shekaru 63 cikin lafazai masu dadi da kanbamawa.

A cikin takardar, mai dauke da sa hannun Simon Lalong, gwamnan jihar Filato, NGF ta bayyana Jonathan a matsayin gwarzo, wanda ya jawowa Najeriya kima da mutunci a idon duniya.

Kazalika, shugaba Buhari ya aika sakon taya Jonathan murnar cikar shekaru 63 da haihuwa, inda shi ma ya bayyana shi a matsayin gwarzo kuma dan kishin kasa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here