Arewa: Gwamnonin Sun Sha Alwashin Tabbatar da Hadin Kan Najeriya
A ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba gwamnonin arewa suka yi wani taro a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.
Ba gwamnoni kadai suka je taron ba, ministoci, manyan sarakuna, jami’an tsaro da sauran manyan mutane a arewa sun samu halarta – Sun tattauna a kan duk wasu matsalolin arewa kamar zanga-zanga, ASUU, kafafen sada zumunta da yadda za’a shawo kansu.
A ranar Litinin gwamnonin arewa suka yi kushe a kan zanga-zangar EndSARS, da kuma sauran al’amura da za su tayar da tarzoma, inda suka ce duk wanda ke neman canji bayan zabe to yayi zanga-zangar lumana. Gwamnonin sun roki mutane da su hada kai da nuna kaunar juna tsakanin ‘yan Najeriya, Vanguard ta ruwaito.
Read Also:
Sun fadi hakan ne a wata takarda da shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya karanta bayan wani taro da suka yi a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.
Sakataren gwamnatin tarayya, shugaban ma’aikatan shugaban kasa, ministoci, sarakunan arewa da sauran manyan mutane sun samu damar halartar taron.
Takardar da aka rubuta a ranar 2 ga watan Nuwamba ta kunshi abubuwa da dama wadanda za a yi don kawo cigaba a arewa.Inda suka mika jinjinarsu ga shugabannin gargajiya a kan babbar rawar da suka taka wurin dakatar da matasan arewa daga yin zanga-zangar EndSARS.
Sun tattauna yadda za su kawo hadin kai da cigaba a kasa. Sannan sun tattauna a kan yadda mutane ke yada labaran bogi a kafafen sada zumuntar zamani. Sun tattauna a kan yadda za a sanya ido a babban birnin tarayya don gudun cigaba da lalata dukiyoyin gwamnati.
Sannan sun shawarci majalisar dattawa da su dinga hanzarin dakatar da duk wata zanga-zanga a cikin kasa. Kuma sun tattauna bukatar yin gaggawar daidaitawa da ASUU don dalibai su koma makarantunsu.