Dalilin da Yasa Gwamnonin APC Suka Hana Buhari Zama da ‘Yan Majalisar Tarayya
Gwamnonin jam’iyyar APC basa son shugaba Buhari ya zauna da ‘yan majalisar tarayya a kan harkar tsaro.
A cewar gwamnonin, matsawar ya zauna dasu zai janyo raini gare shi, su dinga bukatar zama dashi a kan kananun abubuwa.
Gwamnonin sun yanke shawarar zaunawa da ‘yan majalisun jihohinsu, amma babu tabbas idan har da ‘yan jam’iyyun adawa.
A kan taron APC NEC, gwamnonin jam’iyya mai mulki sun yi wani taro a ranar Litinin da yamma, inda suka tattauna a kan makasudin taron da za a yi na NEC.
A taron, Premium Times ta gano cewa gwamnonin sun hada kai a kan hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zaunawa da ‘yan majalisar tarayya a kan batun rashin tsaron da ke kasar nan.
Read Also:
Sun ce hakan zai iya janyo wa shugaban kasa raini, ta yadda ‘yan majalisar tarayya za su dinga kiransa taro a kan kananun abubuwa.
Sannan sun ce za su tayar da wannan maganar a taron NEC da za su yi. Gwamnan jihar Ondo, Mr. Akeredolu, ya nuna amincewarsa a kan wannan batun.
NEC ta kawo wannan shawarar, sannan ta umarci gwamnoni da su zaunar da ‘yan majalisar jihohinsu su tattauna dasu a kai.
Ga dukkan alamu gwamnonin APC za su yi taro da ‘yan majalisar tarayya. Amma ba a san me za su tattauna ba a taron.
Ba a kuma san ko za su gayyaci sauran yan majalisar da ke karkashin jam’iyyun adawa ba, ko kuma menene makomarsu saboda canja shawarar.
An yi kokarin neman Yekini Nabena, mataimakin kakakin jam’iyyar APC na kasa, don jin ta bakinsa, amma abin ya ci tura don bai amsa kiran da aka yi masa ta waya ba, kuma bai mayar da martani a kan sakon da aka tura masa ta waya ba.