Sako Igboho: Gwamnonin Yankin Yarbawa na Aiki Bayan Fage – Gwamna Sanwo-Olu
Gwamnan Jahar Legas ya ce gwamnonin yankin Yarbawa na kai gwauro da mari wajen ganin an sako Sunday Igboho.
Ya ce ba lallai ne sai sun fito fili sun bayyana wa jama’a kokarin da suke yi na a sako Igbohon ba.
An kama Sunday Igboho ne ranar Litinin a filin jiragen sama a Cotonou.
Read Also:
Gwamnan Jahar Legas, Babajide Sanwo-Olu a ranar Asabar ya ce gwamnonin Kudu maso Yamma suna aiki ta bayan fage wajen ganin an saki mai ikirarin fafutikar ‘yancin Yarbawa, Sunday Igboho.
An kame Igboho ne a Cotonou na Jamhuriyar Benin ranar Litinin da ta gabata yayin da yake shirin shiga jirgi zuwa Jamus.
Gwamna Sanwo-Olu, wanda ya amsa tambayoyin manema labarai an tambaye shi abin da gwamnonin Kudu maso Yamma ke yi wajen ganin an sako Igboho, rahoton PMNews.
Gwamnan ya amsa cewa da Gwamnonin yankin suna aiki ta bayan fage domin sakin nasa.
Ya ce gwamnonin ba za su iya zuwa ga jama’a su sanar da abin da suke yi a kan batun Igboho ba.