Biafra: Gwanda Ballewa Daga Najeriya Akan Yakin Basasa – Ambasada Yerima Abdullahi
Ambasada Yerima Abdullai yace gwanda a bari Igbo su kafa tasu kasar maimakon tada tarzoma.
Tsohon Jakadan Najeriyan zuwa Malaysiya kuma dattijo yace Najeriya ba zata juri wani yakin basasa ba.
Ya gargadi masu rajin kudu maso gabas suyi nazari kan illar abinda suke nema.
Gombe – Wani tsohon jakadan Najeriya zuwa Malaysiya, Ambasada Yerima Abdullah, ya yi kira ga masu rajin ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biyafara suyi nazari kan illar ballewar Najeriya.
Abdullahi, wanda makusancin Buhari ne, ya ce zai fi kyautata masu rajin su nemi zaben raba gardama saboda hakan zai fi kyau don zaman lafiya da cigaban kasar.
Gwanda Ballewa daga Najeriya da yakin basasa
Read Also:
Ya bayyanawa jaridar Punch a hirar da tayi da shi ranar Talata, 10 ga Agusta cewa:
“Wannan abu ne da muka yi yakin basasa kansa kuma mutane da yawa cikinmu suka mutu, wasu kuma sun rayu. Wasu daga cikin shugabanninmu na da hankali, yawanci sun bayyana cewa ba mu bukatar wani yaki, kuma na yarda da hakan.”
“Amma idan akwai mutanen da ke ganin suna son nasu kasar. Biyafara ko wata kasa, abunda yafi dacewa shinemu basu daman zabe. A yi zaben raba gardama, idan suna son tafiya a barsu su tafi.”
Abdullahi ya bayyana illar da ballewa za ta yiwa yan kasuwan Igbo saboda suna baje a dukkan sassan kasar.
Yace:
“Ya kamata su sani cewa akwai Inyamurai masu arziki a Gaboro a Borno, da kuma Ilela a Kawoje, jahar Kebbi.”
“Akwai Igbo a fadin kasar nan kuma masu arziki ne. Saboda haka kawai a basu dama su tafi mu huta.”