Gwamnatin Tarayya ta Ware N1.13bn domin Aikin Gina Hanyoyi a Fadin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta ware makudan kudade domin aikin gina hanyoyi a fadin Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana aikin da cewa, dukkan jahohin kasar za su ci gajiyarsa ciki har da FCT.
Ministan Ayyuka da Gidaje ya bayyana ana bukatar karin wasu kudaden don cimma burin Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta ce ta ware N1,134,690,048,000.76 a matsayin babban kason farko na gina hanyoyi 12, The Nation ta ruwaito.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Mista Babatunde Fashola, wanda ya bayyana haka, ya ce an zabi hanyoyin ne domin tabbatar da shiyyoyin siyasa shida na kasar sun ci gajiyar aikin.
Read Also:
Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya tuni ta fara aiwatar da kwangiloli sama da 700, wadanda suka hada da gyara da sake gina hanyoyi sama da kilomita 13,000 da gadoji a fadin jahohi 36 na tarayyar kasar da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Fashola ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da bayani ga Ma’aikatar Gudanarwa da Ci Gaban Manyan Hanyoyi, inda ya ce sakamakon girman aikin, akwai bukatar kudade don daukar nauyin ayyukan don kammalawa da kuma kula da su.
Har ila yau, akwai bukatar samar da kudaden gudanar da wasu ayyuka na hadin gwiwa kamar gadoji masu daukar nauyi, gidajen ajiye motocin daukar kaya da sauran kayayyakin da suka fi dacewa da shirin kasuwanci na kamfanoni masu zaman kansu, in ji Ministan.