Gyara Bututun Man Fetur: Kamfanin Man Fetur na NNPC ya Kashe Kuɗi Kimanin N53.36bn
Kamfanin man fetur na ƙasa NNPC ya fitar da rahoton dake nuna kashe kuɗaɗe kimanin 53.36 biliyan wajen gyara bututun man fetur.
Kamfanin ya fidda jadawalin yawan fasa bututun na kowanne wata har tsawon watanni 11 da kuma kuɗaɗen da aka kashe don gyara a watannin.
Daraktan dake kula da bututun ta ƙasa tace an yi haka ne dan kasan cewa a shirye idan aka gyara matatun mai na ƙasa. Kamfanin man fetur na NNPC ya bayyana cewa ya kashe kuɗi kimanin 53.36 biliyan wajen gyaran bututun man fetur a cikin watanni 11.
A cewar kamfanin masu satar man fetur a ƙasar nan na cigaba da ɓannata bututun man fetur ɗin wanda hakan ke saka NNPC cikin wani yanayi mara daɗi.
A rahoton da kamfanin ya fitar na wata-wata yace, haɗin guiwar da suka yi da mutanen wasu yankuna da kuma masu ruwa da tsaki ya fara haifar da ɗa mai ido, domin anfara samun sauƙin fasa bututun man fetur ɗin.
Read Also:
A watan Disamban shekarar da ta gabata an fasa bututu 43, hakan ya nuna samun ƙaruwar fasa bututun idan aka haɗa da na watan Nuwamba da aka fasa guda 35.
Hakanan kamfanin ya bayyana a rahoton sa cewa sauran watannin da aka fasa bututun sun haɗa da; Watan Oktoba an fasa guda 23, 21 a watan Satumba, 37 a Agusta, 36 a Yuli, da kuma 33 a watan Yuni.
Sauran watannin kuma anfasa bututu 37 a watan Mayu, 65 a Afrilu, 19 a Maris, 32 a Fabrairu, da kuma guda 60 a watan Janairu, jaridar Punch ta ruwaito.
Haka nan kuma rahoton kamfanin ya bayyana kuɗaɗen da aka kashe wajen gyara wuraren da aka fasa bututun na kowanne wata.
An kashe 5.48 biliyan wajen gyaran bututun a watan Janairu, 6.74 biliyan a Fabrairu, 7.69 biliyan a Maris, 7.84 biliyan a Afrilu, 7.99 biliyan a Mayu, da kuma 6.24 biliyan a Yuni.
An kashe 1.80 biliyan a Yuli, 1.49 biliyan a Agusta, 4.49 biliyan a Oktoba, da kuma 6.38 biliyan a Nuwamba.
Sai dai ba’a yi wani gyara ba a watan Satumba.
Daraktan dake kula da bututun man fetur da wurin ajiyar su ta ƙasa, Mrs Ada Oyetunde, ta ce anyi waɗannan gyare gyaren ne don bututun su kasance a shirye wajen gudanar da aiki idan aka gyara matatun man fetur ɗin ƙasar nan.