Mun Kawo Muhimman Tsare-Tsare Domin Gyara Kura-Kuran Baya – Ministan Yaɗa Labarai

 

 

Gwamnatin Najeriya ta ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauki wasu matakai da tsare-tsare ne domin gyara wasu kura-kuran da aka tafka a baya domin dawo da tattalin arzikin Najeriya da ƙarfinsa.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja a wata ganawa da ya yi da ƴan jarida domin bayyana yadda ƙasar za ta yi bikin cika shekara 64 da ƴancin kai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

“A ƙarƙashin mulkin shugaba Tinubu, mun kawo wasu muhimman tsare-tsare domin gyara kura-kuran da aka yi a baya, tare da dawo da martabar Najeriya musamman a ɓangaren tattalin arziki.”

“Duk da matsalolin da aka samu da wahalhalun da ƴan ƙasar suka shiga a sanadiyar matakan, shugaban yana cigaba da ƙoƙarin inganta tattalin arzikin ƙasar da sanya ta a hanya mai ɗorewa da kowa zai ji daɗi.”

Ministan ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka hana ƙasar cigaba shi ne hana ƙananan hukumomin ƙasar sakat, amma shugaban ƙasa Tinubu ya ba su ƴanci domin kai romin dimokuraɗiyya kowane lungu da saƙon ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here