Habasha: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Wasu Mutune a Jihar Oromo

Mahara sun kashe akalla mutun 32 tare da kona gidajen da dama a wani mummunan hari a yammacin Habasha.

Hukumomi sun daura alhakin harin kan kungiyar yan tawaye ta Oromo Liberation Army a jahar Oromo.

Wadanda su ka gane wa idonsu al’amarin sun ce baya ga kisan gomman an kuma sace dabbobi.

Firanminista Abiy Ahmed na da ra’ayin cewa harin harin na da alaka da kabilanci

Hare haren masu nasaba da kabilanci sun karu tun bayan hawan Mr Abiy mulki a watan Afrilun 2018.

Dama kungiyar Oromo Liberation Army ta yi kaurin suna wurin satar mutane don neman kudin fansa da kuma kai hare haren bama-bamai a yammaci da kuma kudancin Habasha.

Wani jami’i ya shaida wa BBC cewa an tura wata tawaga zuwa gundumar Guliso inda harin ya faru don gudanar da bincike.

Hukumomi na fargabar adadin mutanen da a ka kashe a harin sun haura 32.

To sai dai wani wanda ya tsira da ransa ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa jami’an tsaro ba su jima da barin yankin ba maharan su ka zagaye fararen hula.

Ya kara da cewa ‘bayan sun yi mana zobe daga nan kuma sai su ka bude muna wuta.

‘Bayan haka kuma sun sace mana shanu su ka kuma kona mana gidaje.’

Firanminista  ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ‘ ya kadu sosai da karuwar hare-hare masu nasaba da kabilanci da a ke samu a Habasha.’

Ya kuma kara da cewa tuni a ka fara daukar mataki kan maharan.

A watan Yuni an samu barkewar rikicin kabilanci a Habasha biyo bayan kisan sanannen mawakin Oromo Hachalu Hundessa, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutun 150.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here