Hadimin Mataimakin Gwamnan Kwara, Kehinde Obafemi ya Riga mu Gidan Gaskiya

 

Kehinde Obafemi, hadimin mataimakin gwamnan jihar Kwara, Kayode Alabi, ya riga mu gidan gaskiya ranar 30 ga watan Oktoba, 2022.

A wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan ya fitar, Alabi ya kaɗu da jin labarin rasuwar hadiminsa farat ɗaya

Kayode Alabi ya yi wa marigayin Addu’a kuma ya roki Allah ya ba iyalansa da abokanan arziki kwarin guiwar jure rashinsa.

Kwara – Mataimakin gwamnan jihar Kwara, Kayode Alabi, ya yi rashin babban hadiminsa, Kehinde Obafemi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan, Modupe Joel, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, 2022.

A cewar Sanarawan, mataimakin gwamna Alabi ya kaɗu da samun labarin rasuwar hadiminsa ba zato ba tsammani.

Bayanai sun nuna cewa mamacin ya rasu ne ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, 2022 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya. Ya yi Addu’a ga mamacin tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa.

Sanarwan tace:

“Mataimakin gwamna, Mista Kayode Alabi, ya ayyana mutuwar farat ɗaya ta shugaban hadimansa, Kehinde Obafemi, da wani abu da ya sa shi kaɗuwa ba tare da tsammani ba.”

“Mista Kahinde Obafemi, ya rasu ne a ranar 30 ga watan Octoba, 2022 bayan fama da rashin lafiya ta kankanin lokaci. Har zuwa ƙarshen rayuwarsa ya kasance ‘Chief Detail’ ga mataimakin gwamnan jihar Kwara.”

Alabi ya miƙa ta’aziyya ga iyalai Mista Alabi ya yi Addu’ar Allah ya jikan mamacin tare da Fatan samu kwarin guiwar jure wannan rashin ga iyalansa da kuma abaokanan arziki.

“Mista Alabi ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mariyagi Kehinde Obafemi kuma ya bai wa iyalansa, Abokanai da makusantansa kwarin guiwar jure wannan babban rashida suka yi,” inji Sanarwan.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here