Sabbabin Hafsoshin Tsaro Sun Ziyarci  Jahar Borno

 

Sabbin hafsoshin sojojin da shugaba Muhammadu Buhari ya nada sun isa jahar Borno a ranar Lahadi.

An bayyana cewa hafsoshin sun isa garin Maiduguri domin zaman tattauna yadda zasu bullowa ta’addanci a yankin.

Hafsoshin zasu kuma zauna da masu ruwa da tsaki a yankin don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Sabbin hafsoshin sojan Najeriya sun isa Maiduguri, babban birnin jahar Borno tare da niyyar ganawa da masu ruwa da tsaki don shawo kan yadda za a magance tayar da kayar baya a fagen daga.

Babban hafsan hafsoshin tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ya jagoranci shugabannin hafsoshin zuwa hedikwatar rundunar tsaro ta rundunar Operation Lafiya Dole da ke Maiduguri da misalin karfe 1:30 na rana a ranar Lahadi.

Wata babbar majiyar tsaro da ta bayyana wa wakilin Daily Trust ta bayyana cewa shugabannin rundunonin tare da sauran masu ruwa da tsaki ana sa ran za su yi tunani da sake dabarun yadda za su bullo da wata hanyar da za ta tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Daily Trust ta ruwaito cewa dukkanin shugabannin hafsoshin da aka nada kwanan nan sun halarci taron.

Ciki har da Shugaban hafsan hafsoshin tsaro, Manjo Janar Leo Irabor; Shugaban hafsan soji, Manjo Janar Ibrahim Attahiru; Shugaban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Awwal Gambo da shugaban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Isiaka Amao duk sun halarci taron.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here