Ba Zamu Halarci Tattaunawar Sulhu ba – Ƴan Tawayen M23
Mayaƙan ƴan tawayen M23 sun ce ba zasu shiga shirin tattaunawar sulhu da gwamnatin Jamhuriyar Dimokardiyyar Kongo ba, wanda za ayi a yau Talata a ƙasar Angola bayan da Tarayyar Turai ta sanyawa mambobin ƙungiyar sabbin takunkumai.
A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta M23 ta zargi wasu cibiyoyin ƙasashen duniya da ba ta bayyana sunansu ba, da yin zagon ƙasa ga yunƙurin samar da zaman lafiya.
Read Also:
Jagoran ƙungiyar ta M23 Bertrand Bisimwa na cikin waɗanda aka sanyawa takunkumi.
Tun da farko Rwanda ta katse duk wata hulɗar diflomasiyya da Belgium a kan taƙaddamar da suke yi kan cewa Rwandan na goyon bayan mayaƙan ƴan tawayen M23.
Sai dai ministan harkokin wajen Belguim Maxime Prevot ya shaidawa BBC cewa matakin na Rwanda ba shawara ce mai kyau ba, saboda za ta yanke duk wata hulɗar diflomasiyya tsakaninsu.
A ɗaya ɓangaren, gwamntin Kongo ta ce zata halarci tattaunawar duk da wannan koma baya da aka samu.