2023: Halaye 8 da Ya Zama Dole Magajin Buhari ya Mallaka – IBB

 

Ana iya cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), tsohon shugaban kasar Najeriya, yana da karfi idan aka zo batun siyasa a kasar.

Yayin yakin wanda zai gaji shugaba Muhamadu Buhari bayan karewar wa’adin mulkinsa a 2023 ke kara karfi a tsakanin mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP), kalaman dan siyasan na iya kawo cikas ga wasu.

A wata hira ta musamman da Arise TV a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta, tsohon shugaban mulkin sojin ya gargadi ‘yan Najeriya akan zabar wani tsohon dan siyasa don ya gaji shugaba Buhari a babban zabe mai zuwa.

Sai dai, ya ba da shawara da a zabi matashi kuma mai kuzari wanda bai wuce shekaru 60 da haihuwa ba don zama shugaban ƙasa na gaba.

A nan Legit.ng ta gabatar da halayen da IBB ya ce ya zama dole matashin ɗan siyasar da ke son ya gaji Buhari a 2023 ya mallaka:

1. Dole ne kada dan takarar shugaban kasa ya haura shekara sittin

2. Dole ne ya fahimci manyan matsalolin kasar

3. Dole ne dan takarar da ya dace ya zama jagoran Najeriya nagari

4. Dole ne ya kasance mutum da yi tafiya sosai a duk fadin Najeriya

5. Dole ne ya kasance yana da abokai a ko’ina

7. Dole ne ya kasance ɗan siyasa nagari

8. Ya kamata ya iya yin magana da ‘yan Najeriya

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here