Hukumar Lafiya ta Duniya ta Bayyana Cutar da ta fi Kashe Yara a Duniya
Hukumar lafiya ta duniya ta ce cutar sanyi ta Nimoniya ita ce a gaba a cikin jerin cututtukan da ake dauka, wanda kuma ya fi kashe yara a duniya.
A cewar hukumar yara sun fi hadarin kamuwa da cutar ne, saboda garkuwar jikinsu ba ta da karfi.
Hakan yasa jikinsu ba ya iya yakar kwayoyin cutar da ke haddasa cutar.
Haka kuma likitoci sun bayyana wasu cututuka da cewa idan yaro ya yi su ta zai iya kamuwa da cutar ta nimoniya.
Cututtukan sun hada da kyanda da tarin shika da kuma yaran da a kan haifa da rami a zuciya.
Alkaluman WHO sun nuna cewa, a shekarar 2017 kacal, cutar ta kashe akalla yara ‘yan kasa da shekara biyar fiye da dubu 808.
Haka kuma cutar sanyin tana addabar mutanen da shekarunsu suka haura 65 a duniya.
Cutar ta fi kamari ne a kudancin Asia da kuma yankin hamadar saharar Afrika. In ji hukumar.
Cutar dai na yaduwa ne ta hanyar dauka kai tsaye daga wani wanda ke fama da ita zuwa wani.
WHO ta wasu hanyoyin da ake daukar cutar, sun hada da ta hanyar tari ko atishawa daga mai fama da cutar sanyin.
Sannan kuma ana iya daukar nimoniya ta hanyar jini, a wajen haihuwa.
Yaran da cutar ta yi kamari a jikinsu ba sa iya ci ko sha, sannan su kan fita hayyacinsu, jikinsu ya yi sanyi kalau kuma suna yin jijjiga.