Gwamna Zulum ya Bayyana Halin da Borno ta ke Ciki Saboda Mika Wuyan ‘Yan Boko Haram

 

Borno – Gwamnan Borno, Babagana Zulum, yace jahar Borno ta shiga wani mawuyacin hali saboda mika wuyan da mayakan Boko Haram ke yi.

Gwamnan yace lamarin yana bukatar kulawa daga masu ruwa da tsaki da wakilan yankunan da lamari, ya shafa domin su haɗa kai a nemi hanyar warware damuwar.

Zulum ya faɗi haka ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook, yayin ziyarar da yakai garuruwan Bama da Gwoza ranar Asabar.

Me yakai Zulum Bama da Gwoza?

Gwamna Zulum yakai ziyara waɗannan garuruwa ne domin aikin jin kai da kuma duba cigaban da aka samu.

Kafin daga bisani ya yi jawabi ga jami’an sojojin Bama da Gwoza, shugabannin yanki a fadar sarkin Gwoza da Shehun Bama.

Gwamna Zulum ya yi jawabi iri ɗaya a dukkan garuwawan biyu, inda yace:

“Mu a jahar Borno muna cikin mawuyacin hali, dole ne mu zaɓi ɗaya cikin abu biyu masu wahala, kodai mu zaɓi yaƙi da yaki ci yaki cinyewa ko kuma mu amince da yan ta’adda dake mika wuya suna son dawowa cikinmu.”

“Abu ne mai matukar wuya garemu musamman waɗanda suka rasa yan uwansu da sojojin da suka rasa abokan su, su iya rungumar waɗannan tubabbun mayakan har mu rayu tare da su.”

“Babu wanda zai iya cigaba da rayuwa da wanda ya kashe mahaifansa ko wasu yan uwansa, masoyansa a wuri ɗaya.”

Ina babbar matsalar take? Gwamnan yace amincewa da yan Boko Haram yana tattare da hatsarin bata wa wasu rai, waɗanda aka kashe yan uwansu, kuma suna iya yin bore.

A ɗaya bangaren kuma, Zulum yace kin Amincewa da su ka iya sanya su jone da maƴakan ISWAP su kara musu karfi.

Gwamna bayyana cew zai tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari da manyan hafoshin tsaro da shugabannin al’umma da malaman addini.

Hakanan yace zai tatattuna da ƴan majalisar wakilai da malaman makaranta da sauran masu ruwa da tsaki musamman waɗanda lrikicin Boko Haram ya shafa don ganin an samo mafita a wannan lamari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here