Hamas ta Harba wa Isra’ila Rokoki Uku

 

Hamas ta ce ta harba rokoki uku zuwa Isra’ila daga Gaza.

Sai dai Isra’ilar ta ce ta kakkaɓo ɗaya daga ciki sannan babu wanda ya jikkata.

A wani labarin, rundunar sojin Isra’ila ta gargadi Falasɗinawa da su kaucewa babbar hanyar shiga Gaza.

Rundunar ta ce ta jibge dakarunta kan babbar hanyar da ta haɗa arewaci da kudancin Gaza.

Kafar watsa labaran Isra’ila ta ruwaito cewa wanann wani sabon umarni ne ga Falasɗianwa da su janye daga arewaci zuwa kudancin Gaza.

Ma’aikatar lafiya ta Gaza da Hamas ke jagoranta ta ce aƙalla Falasɗinawa 600 aka kashe cikin hare-haren da Isra’ila ta kai Gaza cikin kwanaki uku.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here