Corona: Dokar Hana Shiga Ofis Kan Cutar a Najeriya na Tayar da Hankali
Bayan da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa daga ranar daya ga watan Disamba duk wani ma’aikacin gwamnatin ba za a bar shi ya shiga ofis ba sai ya nuna shedarsa ta yin rigakafin corona ko kuma shedar ba ya dauke da cutar, ma’aikata da dama na bayyana ra’ayoyin daban-daban.
Sakataren Gwamnatin wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da shugaban kasar ya kafa kan yaki da corona Boss Mustapha ne ya sanar da matakin a yayin zaman ƴan kwamitin a Abuja ranar Laraba 13 ga watan Oktoba 2021.
Jaridar Daily Trust ta ambato wani bangare na sanarwar na cewa ” daga ranar 1 ga watan Disambar 2021, gwamnatin tarayya za ta bukaci ma’aikatanta su nuna shaidar cewa an yi musu allurar rigakafi ko kuma sakamakon da ke nuna cewa ba su dauke da cutar wanda bai wuce sa’a 72 ba kafin su shiga ofis.”
A cewar Sakataren Gwamnatin, kididdigar gwaji ta sama da makonni hudu da suka wuce ta nuna cewa yayin da bazuwar cutar ke raguwa a wasu jahohi, tana karuwa ne a wasu jahohin.
Ga ra’ayoyin wasu daga cikin ma’aikata sa dai mun sakaya sunayensu;
Daga jahar Jigawa wannan cewa ya yi, ”matakin ya yi tsauri, mutane abin da suke fama da shi yanzu shi ne albashi kansa ba ya isar ma’aikata.
“Kuma tuni ai daman matakin da gwamnti ta dauka cewa ma’aikacin da yake daga mataki na 12 zuwa kasa kada ya je aiki, idan dai harkar korona ake magana ai ya isa ya yi magani tun da korona ba ta son cudayya to wannan matakin kadai ya isa, to kuma har a ce sai ka je ka yi wannan allura idan babu ita ba za ka je ofis ba wannan matakin ya yi tsauri gaskiyar magana.
“Kuma zai iya kara sawa mutane hankalinsu ya sake barin gwamnatin gaba daya.”
Daga Abuja: “Tun da dai matsala ce wadda ta shafi duniya baki daya ta wannan annoba ta corona ko da yake ita gwamnatin tana so ta yi amfani da wadanda take da iko a kansu, kasancewar wasu jahohi sun yi kokarin su sa a yi amma aka samu tirjiya wannan mataki zai sa a samu mutane da yawa da za su yi rigakafin.
To amma gaskiya gwamnati kamata ya yi ta wayarwa da mutane kai sosai a kan allurar domin har yanzu mutane da dama har ma da ƴan Boko kar ka yi mamaki wadanda suke nuna shakku ko ma zargin cewa rigakafin yana da lahani zai jawo kaza zai jawo kaza. Ko da yake ni na riga na yi nawa.”
Wata ma’aikaciya daga Abuja cewa ta yi, ” Ina ganin ba abu ne da ya zama dole ba, domin hukumar lafiya ta duniya ta riga ta ce allurar rigakafin ba dole ba ce.
“Idan dai har suna son su sa mutane su yi rigakafin ne to bai kamata su tilasta wa mutane su ce lalle sai an yi ba. Mutane da yawa kowa yana da dalilin da ya sa bai yi ba.
“Idan gwamnti ta ce lalle kowa sai ya yi to ta shiga hakkin mutane. Ni dai a yanzu ban yi b kuma ban san abin da zan yi ba idan lokacin d gwamnatin ta yi ya zo.
“Ina fatan lamarin da ba zai kai a ce gwamnati ta tilasta yin allurar ba. Ina fatan za ta sauya shawara kafin lokacin. Kuma ma allurar har guda nawa ake da ita a Najeriya, da za a tilasata wa jama’a?
“Ai allurar ma babu ita wadatacciya a kasar. Gwamnatin ba ta ma shirya wa bin da take magana a kai ba.”
Wannan kuwa cewa take; “Eh to yana da kyau in dai har zai zama matakin kawo karshen yaduwar cutar coronar ina ganin ya dace tun da har yanzu gwamnati ba ta bayar da umarnin ma’aikata ƴa matakin 12 zuwa kasa su koma aiki ba.
“Ina ga duk yana daga cikin abin da ya sa ba su bari kowa da kowa ya koma aiki ba.
Amma idan har matakin zai zama silar da za ta sa kowa ya koma bakin aiki kuma ya samu kariya daga cutar hakan yana da kyau. Tun da gwamnati ta ce akwai allurar kuma har yanzu ana kan kawowa abu ne da kowa ya kamata ya yi.
“Tun da dai an ga cewa ba wai yana da wata illa ba. Yawancin wadanda suka yi ba wata matsala ce ta samesu da za a ce rigakafin ne ya sa mu in ban da yan kananan matsaloli wadanda ko da ma ba rigakafin ba mutum yana iya samunsu,” in ji ta.
Martanin shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya
Shugaban kungiyar likitoci ta Najeriyar Dr Uja ya yaba da matakin yana cewa umarnin na gwamnati mataki ne da ya dace wajen yaki da cutar ta corona, inda ya kara da cewa abu da ya shafi bukatar kasa da kuma kulawa.
Ya ce akwai bukatar ƴan Najeriya su kare kansu, yana mai karin bayani da cewa umarnin da shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan yaki da cutar wato Boss Mustapha, kyakkyawan mataki ne na yaki da cutar, wanda kuma ya yi hakan ne ba domin wata muguwar manufa ba, alheri yake nufi da kasar, kamar yadda shugaban kungiyar likitocin ya ce.
Ya ce hakan ya nuna cewa lalle cutar gaskiya ne akwai ta kuma tana nan a tsakanin ƴan Najeriya sosai.
Zuwa yanzu Najeriya ta samu alkaluman mutane 208,404 da suka kamu da cutar ta corona, da kuma wadanda suka mutu 2,761.
Kasar ta kuma yi wa mutane miliyan biyar daga cikin miliyan 200 rigakafin cutar da magungunan Moderna (MRNA.O) da AstraZeneca (AZN.L) daga wadanda ta samu daga shirin samar da rigakafin na kasashe masu tasowa, COVAX
Haka kuma kasar ta samu allurar rigakafin Johnson & Johnson (JNJ.N) miliyan 1.12 da ta saya daga shirin kungiyar kasashen Afirka kuma tana shirin karbar miliyan 7.7 na Sinopharm (1099.HK) ta hanyar COVAX.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here