Yajin Aikin ASUU: Hana Yaran mu Zuwa Makaranta Abu ne Mai Haɗari –  Nwobodo

 

Shugaban hukumar kwadago na kasa, NLC, reshen Jihar Enugu ya ce wasu daliban Najeriya sun zama masu garkuwa da mutane.

Virginus Nwobodo, ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci mambobin NLC da suka yi zanga-zangan goyon bayan ASUU suka tafi gidan gwamnatin Enugu.

Nwobodo ya bukaci Gwamna Ifeanyi Uguwanyi ya mika kokensu ga Shugaba Muhammadu Buhari ya duba batun yajin aikin ASUU ya biya musu bukatunsu don yara su koma makaranta.

Jihar Enugu – Hukumar Kwadago ta Najeriya, NLC, reshen Jihar Enugu, a ranar Talata ta shiga yajin aikin goyon bayan ASUU da ake yi a kasar.

ASUU da sauran kungiyoyi a bangaren ilimi sun shiga yajin aiki kan rashin amincewa da yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da gwamnati.

Duk da cewa yajin aikin an fara shi ne na gargadi na mako hudu, ASUU ta cigaba da tsawaita yajin aikin duk lokacin da wa’adin gargadin ya kare.

Masu zanga-zangan, karkashin jagorancin shugaban NLC na jihar, Virginus Nwobodo, sun tafi gidan gwamnatin Jihar Enugu, kuma gwamnan jihar Ifeanyi Uguwanyi da jami’ansa suka tarbe su.

Mr Nwobodo ya fada wa gwamnan cewa sun taho sakatariyar ne domin su roke shi ya mika damuwarsu ga Shugaba Muhammadu Buhari kan yajin aikin ASUU.

Shugaban kungiyar na kwadagon ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya ke watsi da ilimi duk da muhimmancinsa wurin cigaban al’umma, Premium Times ta rahoto.

“Hana yaran mu zuwa makaranta abu ne mai hadari. Wasu daga cikin yaran sun fara garkuwa da mutane. Wasu sun fara aikata laifuka daban-daban,” in ji shi.

“A yanzu da muke magana, yan ASUU suna fushi. An kori mambobinsu da yawa saboda sun kasa biyan kudin gidan haya da sauran kaya.”

Wasu daga cikin masu zanga-zangan da suka yi magana a sakateriya sun nuna fushinsu kan rashin bada muhimmanci da gwamnati ke yi don kawo karshen yajin aiki.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here