Ministan Sadarwa ya yi Hani da Siyar Sababbin Layukan Waya

 

Hukumar sadarwan Najeriya, ta umurci dukkan kamfanonin sadarwa su dakatad da rijistan sabbin layukan waya a fadin tarayya.

NCC ta bayyana hakan ne a jawabin da diraktan yada labaranta, Dr. Ikechukwu Adinde, ya saki ranar Laraba.

Jawabin yace hukumar ta bada umurnin haka ne bisa ga manufar gwamnatin tarayya na duba rumbun wadanda sukayi rijista da kuma tabbatar da cewa kamfanonin na bin ka’idoji da sharruda.

Ta ce ya zama wajibi a dakatad da layukan wayan da ba’ayi rijista ba wajen ayyukan banza.

A cewar jawabin: “Bisa ga manufar gwamnatin tarayya na cigaba da samun nasara wajen rijistan layukan waya, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, ya umurci hukumar ta kaddamar da binciken rumbun rijista.”

“Manufar wannan bincike shine tabbatar da cewa an bin ka’idoji da sharrudan da aka gindayawa kamfanonin sadarwa.”

“Wannan umurni na da muhimmanci saboda yawaitan layukan waya da ba’ayi rijista ba kuma ake amfani da su wajen ayyukan laifi.”

“Saboda haka, ana umurtan kamfanonin sadarwa su dakatad da sayar da sabbin layuka da rijista har sai an kammala bincike.”

“Za’a kwace lasisin duk kamfanin sadarwan da bai bi wannan umurni ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here