Hanyar da Gwamnoni zasu bi Don Magance Matsalar Tsaro – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni su yi aiki da shugabannin gargajiya.
A cewarsa, aiki dasu ne kadai zai bai wa gwamnati damar sanin halin da al’umma take ciki, da labarai a kan ‘yan ta’adda.
Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a wani taro da yayi da gwamnonin jihohi 36, inda suka tattauna a kan halin da kasa take ciki.
A taron da shugaba Buhari yayi da gwamnoni, ya zauna tsaf ya saurari korafi daga yankuna 6 da ke kasar nan, daga bakin gwamnoni, a kan harkokin tsaro da ke addabar kasarnan.
Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Garba Shehu yace, shugaban kasa ya ce, “Wajibi ne gwamnati tayi aiki tare da shugabannin gargajiya.Ya kamata a hada kai dasu don a san ta inda za a bullo wa lamarin.”
Read Also:
Buhari ya ce mulkinsa ya yi kokarin gyara yankunan arewa maso gabas da kudu-kudu, amma yankin kudu-kudu suna cikin mawuyacin hali, Daily Trust ta wallafa.
Kullum ina samun labarin wata baraka da kuma fasa bututun man fetur. Ya kamata a dakatar da satar mai,” inji Buhari.
Yayin da shugaban kasa yake magana a kan al’amarin ta’addanci da garkuwa da mutane a kowanne yanki, ya ce wajibi ne a tabbatar an kare kasa daga ta’addanci.
“Za mu tabbatar sojoji sun kawo karshen duk wasu ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.”
Ya ce dalilin rufe iyakar kasa duk don a kiyaye shigowa da miyagun makamai da kwayoyi ne.
“Amma yanzu haka muna son mu bude iyakokin kasar nan kusa,” a cewarsa.
Shugaba Buhari ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa za su yi iyakar kokarinsu wurin ganin karshen ta’addanci a kasar nan.