An Haramtawa Ma’aikatan Asibiti Yin Kirifto

Jihar Gombe – Hukumomi a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Gombe sun sanya doka game da ‘kirifto’.

Hukumomin sun haramtawa ma’aikata yin ‘kirifto’ ko ‘mining’ lokacin da suke bakin aiki.

Mataimakin daraktan gudanar na asibitin FTH, Adamu Usman Tela shi ya bayyana haka ga jaridar Aminiya.

Tela ya ce hukumomin asibitin sun lura cewa harkar ‘mining’ yana dauke hankulan ma’aikata yayin da suke aiki.

Ya ce hakan yana da tasiri wurin rashin ba marasa lafiya kulawa ta musamman yayin ɗa suke aiki.

Sanarwar ta ce an dauki matakin ne tun kafin fara samun matsalolin salwantar da rayuka saboda matsalar.

“Mun dauki mataki ne domin kare faruwar salwantar rayuwa, domin kula da lafiyar al’umma shi ne mafi muhimmanci.”

– Adamu Usman Tela

Wannan na zuwa ne bayan matasa maza da mata sun rungumi harkar ‘mining’ domin samun na kashewa.

Wasu na ganin ‘mining’ na dauke hankulan mutane da dama musamman a wuraren aikinsu.

Karin bayani na tafe….

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Logged in as Khadija Garba. Log out?

Please enter your comment!