An Harbe Mutane 5 a Wajen ‘Yan Ci-rani a Tripoli

 

Ma’aikatan agaji sun ce akalla mutum biyar aka harbe a wani wuri da ake tsare da ‘yan cirani a Tripoli babban birnin kasar Libya.

Hukumar kula da kaura ta duniya wato IOM ta ce cunkuso ne ya haddasa hargitsi a wurin, daga nan kuma aka soma harbi.

Akwai rahotanin da ke cewa fursononi da dama sun tsere aga cibiyar.

Mahukuntan Libya sun kama ‘yan cirani sama da dubu biyar a baya-bayanan a samamen da suka kai a wurare daban daban da ke birnin Tripoli.

Ma’aikatan agaji sun yi magana akan mutanen da aka lakadawa duka da aka ajiye a cikin mawuyacin hali kurkukun da suka cika makil a wurare da dama.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here