An Sako Chiwetalu Agu

Ƴan fim da dama a Najeriya sun yi Allah-wadai da kama wani fitaccen abokin aikinsu, Chiwetalu Agu, wanda rundunar sojin Najeriya ta kama shi sakamakon saka kaya mai zanne tutar ƴan awaren Biafra.

Sai dai kafar yaɗa labaran Punch ta rawaito cewa an sake shi da safiyar yau.

Rundunar sojin ta ce ɗan fim ɗin yana tunzura mutane mutane su shiga cikin ƙungiyar da ke fafutukar masu son kafa ƙsar Biafra ta IPOB.

Sai dai rundunar sojin ta musanta rahotannin da ke cewa an ci zarafinsa lokacin da aka kama shi a birnin Anaca na jahar Anambra a jiya Alhamis.

Hukumomin Najeriya sun alaƙanta IPOB da kashe-kashen da aka dinga yi a wannan shekarar a yankin kudu maso gabashin ƙasar – inda yawancin waɗanda aka kashe ɗin ƴan sanda ne.

Sai dai ƙungiyar IPOB ta sha musanta zarge-zargen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here