An Jiyo ƙarar Harbe-Harbe Lokacin da EFCC Suka je Kama Yahaya Bello
A daren jiya Laraba ne jami’an hukumar EFCC suka kai samame gidan gwamnatin Kogi da ke Abuja domin kama tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a Unguwar Asokoro da ke Abuja.
An ce turjiya da jami’an tsaron da suke gadin gidan suka nuna ne ya jawo musayar yawu tsakaninsu da jami’an EFCC.
A wani faifan bidiyo da talabijin na Channels ya wallafa a shafinsa na intanet, an jiyo ƙarar harbe-harben bindiga a kusa da gidan.
Read Also:
Kafin wanna, an shiga ruɗani a game da neman tsohon gwamnan da ake yi, in masu magana da yawunsa suka ce ya kai kansa ofishin EFCC domin amsa nemansa da ake yi, ita kuma EFCC ta fito ta ce ba ta san da wannan ba, tana cigaba da nemansa ruwa a jallo.
A watan Afrilu ne EFCC ta sanar da neman Yahaya Bello ruwa a jallo bisa zarginsa da badaƙalar Naira biliyan 80.2.
An taɓa samun irin wannan lamarin a bayan lokacin da jami’an EFCC suka kai samame gidan tsohon gwamnan da ke yankin Wuse domin kama shi, amma gwamnan Kogi mai ci, Usman Ododo ya zo ye tseratar da shi.
Lamarin dai na gaban kotu, duk da cewa har yanzu tsohon gwamnan bai taɓa halartar zaman kotun ba.