Harbo Jirgin Yaƙin Sojoji: Sojojin Saman Najeriya Sun Karyata Bidiyo da ‘Yan ƙungiyar Boko Haram Suka yi
Sojojin saman Najeriya sun musanta iƙirarin ƴan ƙungiyar Boko Haram na harbo jirgin yaƙin sojoji tun daga sama.
Dama jirgin yaƙin ya tafka hatsari kuma ya ɓata ne tun ranar Laraba, 31 ga watan Maris, kamar yadda aka tabbatar.
Saidai ƴan boko Haram sun yi bidiyo suna tabbatar wa da duniya cewa sune suka tafka wannan aika-aikar Sojojin saman Najeriya sun musanta iƙirarin da ƴan ƙungiyar boko haram suka yi a wani bidiyo na harbo jirgin yaƙin sojojin da aka nema aka rasa tun ranar Laraba, 31 ga watan Maris.
Read Also:
Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, Boko haram sun saki wani bidiyo suna tabbatar wa da duniya cewa sune suka harbo jirgin yaƙin.
Sa idai babban jami’in hulɗa da jama’a na sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya musanta maganar wannan bidiyon da ƴan Boko Haram suka saki.
Ya ƙara da tabbatar wa da duniya cewa ƴan Boko Haram sun lailayo wata ƙaryar ne kawai suka maka duk don su ƙara wa labarin armashi amma maganar gaskiya ba haka bane.
Kamar yadda kakakin NAF din, Air Commodore Edward Gibkwet yace:
“Mun ga wasu bidiyoyi suna yawo wadanda babu wata alama da take nuna cewa jirgin namu ne, ko kuma wani matuƙin jirginmu ko kuma alamar jirginmu ne wannan wanda suke nunawa.
“Da alama wani bidiyo ne can daban da aka ɗauka a wani wuri wanda ko shuke-shuken wurin ba na arewa maso yamma bane.
Suna ta sakin bidiyoyin da kadan-kadan kuma muna kallo.”