Hari Kan Motar Bas ya Kashe Mutane 6 a Kamaru

 

Akalla mutum shida suka mutu sannan takwas kuma suka jikkata a wani hari kan motar bas da ake zargin ‘yan bindiga da kaiwa a Kudancin Kamaru jiya Talata.

Kungiyoyin ‘yan aware sun kaddamar da hare-hare na tsawon makonni biyu kan garuruwan mutane da ke magana da turancin ingilishi na Kamaru. Babu dai wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin.

Harin ya shafi wata motar fararen hula wadanda suke tafiya daga Douala zuwa Kumba, inda aka far musu a garin Ekona.

Shugaban asibitin yankin ya fadawa BBC cewa uku daga cikin mutum takwas din da suka jikkata da aka kai asibitin na cikin mawuyacin hali.

Amma ya kara da cewa sun fara samun lafiya bayan aiki da aka musu sannan ana duba lafiyar sauran mutane biyar da harin ya shafa.

Wadanda suka tsira sun ce ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi ta harbin su da kuma dora musu laifin take dokar kulle da kungiyoyin ‘yan awaren suka kafa.

Shugaban kasar ta Kamaru, Paul Biya, ya bayar da umurnin aike da dakaru na musamman zuwa yankin domin tabbatar da ba a samu tarnaki ba wajen sake bude makarantu.

Kungiyoyin ‘yan awaren dai sun saka dokar kulle a arewa maso yamma da kuma kudu maso yammacin Kamaru domin hana yunkurin sake bude makarantu a yankin inda suke fafutukar samun yancin kai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here