Adadin Mutanen da Suka Mutu a Harin da ‘Yan Bindiga Sukai a Kauru, Lera Zangon-Kataf
Miyagu sun kai hara-hare a garuruwan Kauru, Lere da kuma Zangon-Kataf.
An rasa rai a Ungwan Gaiya, Ungwan Gimba, Ungwan Makama da Apimbu.
Gwamnatin Kaduna tace an rasa ran mutum 14 daga Alhamis zuwa Asabar.
Mutane hudu, daga ciki har da wasu makiyaya sun mutu a wani hari da aka kai a cikin wasu kauyukan garin Zangon-Kataf, jihar Kaduna.
A ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, 2020, Punch ta rahoto cewa an yi ta’adi a Ungwan Gaiya, Ungwan Gimba, Ungwan Makama da Apimbu.
Kwamishinan harkoki da tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi da yamma.
Read Also:
Mista Aruwan ya yi wa jawabin da ya fitar take da: “An kashe mutane hudu a harin ramuwar gayya, yayin da aka baza dakaru a wuraren rikici.”
A cewar Kwamishinan, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi kira a bar doka ta yi aikinta.
Tsakanin ranar Alhamis zuwa daren Asabar, ‘yan bindiga sun hallaka akalla mutane 14 a kananan hukumomi uku; Zango-Kataf, Kauru da Lere.
Rahoton yace wadanda aka yi wa rauni suna jinya a asibiti, yayin da aka kona gidaje kurmus.
Kwamishinan yace jami’an sojoji da ‘yan sanda sun tabbatar masu cewa an kai harin ne a matsayin ramuwar gayya na kashe-kashen da aka yi.
A garuruwan Unguwan Idi da Kasheku a karamar hukumar Kauru, an kashe makiyaya bakwai a harin. Bayan nan, an kashe wani mutum a yankin Apimbu.
Jami’an tsaro sun samu gawar mutane uku a Unguwan Gaiya, Ungwan Gimba da Unguwan Makama, ba a iya gane fuskar daya daga cikinsu ba.