Mutane 87 ne Suka Rasa Rayukansu a Harin Bam Din Masallacin Pakistan
Akalla mutum 87 ne suka mutu kawo yanzu a sanadiyar harin bam din da aka kai kan masallata a wani masallaci da ke birnin Peshawar na kasar Pakistan.
Masallacin na cikin yanki mafi tsaro ne kusa da shalkwatar ‘yan sandan kasar Pakistan kuma tuni aka kaddamar da bincike kan yadda dan kunar bakin waken da ya kai hari ya sami kutsawa cikin masallacin.
Read Also:
Firaministan kasar da manyan jami’an gwamnatinsa sun yi tir da harin na ranar Litinin – daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai a kasar cikin shekarun da suka gabata.
Kungiyar Taliban reshen kasar Pakistan ta musanta cewa tana da hannu a harin, bayan da wani kwanadanta ya yi ikirarin su suka kai harin.
Wani kakakin asibitin da aka kai yawancin wadanda harin ya rutsa da su, ya shaida wa manema labarai cewa fiye da mutum 100 sun sami raunuka.
Kawo yanzu an yi jana’izar fiye da ‘yan sanda 20, kuma mutum iye da 100 sun sami raunuka. An kuma mika wa iyalan mamatan yawancin gawarwakin ‘yan sandan da suka mutu.