Bayan Harin Boko Haram: ‘Yan Kauyukan Sun Fara Komawa Gida
Mazauna kauyukan karamar hukumar Hawul da Boko Haram suka ragargaza sun fara komawa gida.
Mayakan ta’addancin sun kai hari kauyukan inda suka kone majami’u biyu a ranar Kirsimeti.
Sun bayyana yadda suka kwana a cikin dajika da tsaunika a yayin gudun ceton ransu yayin harin Daruruwan mazauna kauyukan Shindifu, Kirbutu, Debiro, Shafffa, Tashan Alade da Azare a karamar hukumar Hawul ta jihar Borno sun fara komawa gidajensu don ganin barnar da ‘yan Boko Haram suka yi musu a yammacin Asabar.
Read Also:
Mayakan ta’addancin sun kai hari a lokaci daya yankunan kasa da sa’o’i 48 da suka kai hari garin Garkida da ke jihar Adamawa, Vanguard ta wallafa.
Da yawan mazauna karamar hukumar Hawul Kirisitoci ne kuma tana da nisan a kalla kilomita 200 daga Maiduguri.
A yayin bayyana halin da suka shiga, Mallam James Ishaya, mazaunin garin Shaffa ya ce mayakan ta’addancin sun dauka kusan sa’o’i 10 suna ragargazar jama’a ba tare da dakarun sojoji sun iso ba.
Ya jajanta yadda da yawa daga cikinsu suka tsere daji inda suka kwana a tsaunika tare da iyalansu kafin su fara komawa gidajensu da safe.