Kungiyar ACF ta Bayyana Harin ‘Yan Bindiga a NDA a Matsayin Abun Bakin Ciki
Kungiyar ACF ta yi martani a kan harin da ‘yan bindiga suka kaiwa Kwalejin horon sojoji na Najeriya (NDA).
Kungiyar arewar ta bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki.
Ta kuma nemi a ceto jami’in da aka sace tare da gurfanar da masu laifin.
Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta nuna bacin ranta game da harin da ‘yan bindiga suka kaiwa Kwalejin horon sojoji na Najeriya (NDA), Daily Nigerian ta rawaito.
Da sanyin safiyar Talata, 24 ga watan Agusta ne wasu ‘yan bindiga sun kai hari a makarantar sannan kuma suka kashe jami’anta biyu, inda suka yi garkuwa da daya a cikin lamarin.
Da take mayar da martani a cikin wata sanarwa da kakakinta, Emmanuel Yawe ya fitar, ACF ta ce abin bakin ciki ne cewa “‘yan fashin titi” za su iya mamaye NDA.
Read Also:
Yawe ya ce dole ne a ceto jami’in da aka sace sannan a gurfanar da wadanda suka kai harin, jaridar TheCable ta rawaito.
Ya ce:
“Wadannan manyan jami’ai sun yi gagarumin sadaukarwa ga Najeriya, kasarsu ta asali.
“Muna fatan sadaukarwar su ba ta banza ba ce. Kungiyar tana addu’a don ganin cewa an kubutar da jami’in da aka sace tare da gurfanar da masu laifin da suka sace shi.
“Abin takaici ne ƙwarai da gaske cewa ‘yan fashin titin kawai za su mamaye wani sansanin sojoji na irin wannan babban martaba na ƙasa da ƙasa, su mamaye tsarin tsaro da jami’ai a wurin, su kashe jami’an sannan su tafi da ɗaya zuwa inda ba a sani ba.
“NDA abin tunawa ne mai cike da alfahari da nasarorin da kakanninmu suka samu.
“Mu a ACF mun sha nanatawa cewa akwai matsala game da gudanarwar tsaronmu. A kwanakin baya wasu da ake kira ‘yan fashi ne suka harbo wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya.
“A yau masana’antar da ake samar da dukkan hafsoshin sojojin Najeriya an mamaye ta an lalata ta. Me kuma muke bukata don nuna cewa tsarin tsaronmu na kasa yana aiki ne a baya?”