Mutane 40 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Harin Roka da Falasɗinawa suka kai Isra’ila

 

Hukumomin Isra’ila sun ce mutanen da suka mutu sakamakon harin makamin roka da Falasɗinawa suka kai yankinta ya kai 40.

Jami’an bayar da agajin gaggawa sun ce suna ci gaba da bayar da taimakon lafiya da kuma kai mutane asibiti.

Ma’aikatar lafiya a ƙasar ta Isra’ila ta ce harin ya kuma jikkata mutum sama da 700.

Sai dai hukumomi ba su kai ga tabbatar da alkaluman waɗanda suka jikkata ba kawo yanzu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com