Harin Sansanin Jami’an Tsaro a Zamfara: Rahoto ya Nuna Cewa ‘Yan Bindigan Sun yi Amfani da Damar Rashin Hanyoyin Sadarwa
‘Yan bindiga sun shiga sansanin jami’an tsaro a jahar Zamfara, sun yi barna.
Hakan ya yiwu ne saboda kashe hanyoyin sadarwan da hukumar NCC ta yi.
Duk da hakan ya taimaka, rashin sadarwan ya jawo wa jami’an tsaro cikas.
Zamfara – Daily Trust tace harin da aka kai wa dakarun jami’an tsaro a jahar Zamfara a ranar Asabar ya yiwu ne saboda kashe hanyoyin sadarwa da aka yi.
‘Yan bindiga sun shiga sansanin runduna da ke Mutumji, suka kashe sojojin ruwa tara, sojan kasa daya da wani jami’in ‘dan sanda, sannan suka saci makamai.
Rahoton yace abin da ya faru shi ne miyagun sun yi amfani da damar rashin sadarwa, suka kai harin.
Read Also:
Sojoji ba su da hanyar yin waya
Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa mafi yawan sojoji suna amfani da wayoyin salula ne wajen sadarwa, manyan sojoji ke amfani da wayar oba-oba.
“Ko da toshe layukan wayoyin salula ya taimaka wajen dakile ‘yan bindiga a Zamfara, hakan kuma ya kawo wa sojoji cikas domin babu wata kafar sadarwa.”
“Manyan dakarun sojoji ke amfani da rediyon soja ko salular walkie-talkie, a dalilin haka, jami’an tsaro da ke fagen yaki suna aiki ne da wayoyin salularsu.”
“Yan bindiga sun yi amfani da wannan dama, suka kai masu hari a sansaninsu. Akwai bukatar sojoji su tanadi samu na’urorin sadarwa na musamman.”
Har yau wasu ‘yan bindiga suna iya yin waya ta hanyar amfani da wayoyi irinsu Thuraya ko aiki da layin Airtel da Glo ko kuma su shiga yankunan Sokoto da Kaduna.