Harin 9/11: Ofishin Jakadancin Saudiyya na Amurka ya ƙaryata zargin

 

Saudiyya ta yi maraba da sakin wasu bayanan sirri da suka shafi harin 11 ga watan Satumban 2001 a Amurka a ranar Laraba.

A cikin wata sanarwa, ofishin jakadancin Saudiyya na Amurka ya ce “duk wani zargi cewa Saudiyya na da hannu a hare-haren ranar 11 ga Satumba ƙarya ce kawai.”

Shugaban Amurka Joe Biden a ranar Juma’a ya ba Ma’aikatar Shari’a umarnin sake nazari kan bayanan binciken sirrin da hukumar bincike ta FBI ta gudanar kan harin 9/11 domin tantancewa da kuma sake sakin bayanan.

Iyalan waɗanda harin na 11 ga Satumba ya rutsa da su, su suka buƙaci a sake gudanar da bincike kan zargin FBI cewa ta yi ƙarya ko ta ɓoye shaidar da ke tabbatar da hannun Saudiyya da kuma alƙarta da ƴan bindigar da suka kai harin.

Saudiyya ta ce ba ta da hannu da ƙwace ikon jirgin da ya kai hare -haren.

Ofishin jakadancinta ya ce Saudiyya ce ta yi kira da a sake fitar da bayanan binciken harin na Amurka.

“Kamar yadda binciken da ya gabata ya bayyana … babu wata shaida da ta nuna cewa gwamnatin Saudiyya ko jami’anta suna da masaniya a baya game da harin ta’addancin ko suna da hannu wajen kitsa kai harin,”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here