Harin Bam ya Kashe Mutane 21 a Sudan

 

Wata ƙungiyar likitoci a Sudan ta ce aƙalla mutum 21 ne suka mutu, yayin da wasu fiye da 70 suka jikkata sakamakon luguden wuta a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a kudu maso gabashin Sudan.

Ƙungiyar likitocin ƙasar ta bayyana cewa, dakarun RSF ne ke da alhakin kai harin a birnin Sennar a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta yi Allah wadai da shi a matsayin kisan kiyashi na fararen hula.

Harin na zuwa ne kwana guda bayan da sojojin Sudan suka yi watsi da shawarar da wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar na aikewa da dakarun ƙasa da ƙasa don kare fararen hula.

Dubban mutane ne aka kashe yayin da sama da miliyan 10 suka tsere daga gidajensu tun bayan ɓarkewar yaƙin basasa tsakanin sojoji da ƙungiyar RSF a watan Afrilun da ya gabata, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin matsalolin jin kai mafi muni a duniya.

Tattaunawar zaman lafiya da dama da Saudiyya da Amurka suka shiga tsakani sun gaza kawo ƙarshen rikicin.

Ana zargin ɓangarorin biyu a rikicin Sudan – sojoji da RSF – da laifin aikata ta’asa kan fararen hula.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here